Yan Sanda Sun Cafke Wata Mahaifiya Saboda Yunkurin Kashe Jariri da Guba

FB IMG 1709485484086

Jami’an ‘yan sanda sun kama wata mahaifiya saboda yunkurin kashe jaririnta da ba shi guba da zummar ya sha ya mutu.

Alfijir labarai ta rawaito ‘yan sanda a jihar Legas sun cafke wata uwa da laifin yunkurin kashe yaronta da ba shi da lafiya, ta hanyar amfani da maganin kwari mai guba, “Sniper”.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a ranar Asabar cewa asibitin koyarwa na jami’ar Legas, Idi-Araba, ya kai rahoton yunkurin ga ‘yan sanda a ranar Juma’a.

Ya ce babban jami’in tsaro a asibitin ya kai rahoto ga ‘yan sanda cewa mahaifiyar ta kawo danta mai shekara daya da wata bakwai asibiti domin yi mata magani.

Ya kara da cewa mahaifiyar ta shaida wa wani likita a asibitin cewa ta ba wa yaron mai suna “Sniper” ya sha a ranar Lahadin da ta gabata a lokacin da firgicin ta bai ragu ba.

“Mahaifiyar ta ce ta ba wa yaron maganin ne domin ya huta daga yawan rashin lafiyar da yake Fama.

“Nan da nan aka aika jami’an bincike zuwa asibiti inda suka taras da jaririn yana karbar magani.

“An kai mahaifiyar don bincike bayan yaron ya samu kulawa,” in ji Hundeyin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *