A daidai lokacin da ake gabatar da sallar juma’a, a ranar Juma’ar da ta gabata, sansanin Ƴan gudun hijira na Rundaben- Shuwa da ke kusa da Bauchi, ya sami ibtila’in mummunar gobara da ta laƙume a ƙalla gidaje 20 inda sama da mutane 100 suka tagayyara a sanadiyar tashin wutar wace ta samo asali daga wani gida a sansani.
Alfijir labarai ta rawaito Gobarar wacce ba a san sanadin tashinta ba ta ƙone kafatanin gidajen da ke gun wanda gaba ɗayan su na kara ne da shubci da kuma abincin da aka tanadar mai tarun yawa.
Gidajen wanda ƴan gudun hijiran su suka samar da su a wani makeken fili mallaƙar Hajiya Maryam Abacha da ke gabas da garin Bauchi.
Wakilinmu ya ce Idar da sallar ke da wuya aka ci gaba da aikin kashe gobarar wacce ta ɗauki kusan sa’o’i uku domin ƙoƙarin shawo kanta don kada ta kone garin baki ɗaya.
Shugaban kungiyar Ƴan gudun hijira na Jihar Bauchi Alhaji Buba Musa Shehu ya jagoranci abokan aikin sa da manema labarai domin kai ɗauki da kuma ganewa idonsa asarar da gobara ta tafka.
Wakilinmu ya ce garin Rundaben-Shuwa surƙuƙin loko ne wanda ko da mota ba ko wace ta ke iya shiga ba, ya ce hatta ruwan rijiyoyi da na burtsatse sai da suka kusan karewa a ƙoƙarin kashe gobarar. Haka kuma ya ce ana hasashen kimani kadarori da abinci na kimani sama da miliyan biyu sun ƙone ƙurmus.
A daidai lokacin da ake ƙoƙarin kashe wutar akwai wani magidanci maras lafiya da aka fito da shi kafin wutar ta iso gidansa, amma ganin irin tashin hankalin da suka shiga kafin wane wanna aiki rai ya yi halin sa. Inji wakilin namu.
Sama da mutane 100 suka tagayyara sakamakon gobarar inda wasu suka koma bukkokin ƴan uwa da massalatai don zama da iyalan su kafin su samu wani tallafi.
Malam Bulama Gujja shugaban sansanin Rundaben-Shuwa ya ce sun kai shekara bakwai a sansanin amma basu taɓa samun annobar wuta irin haka ba, inda yawanci abinci da suka noma da kayan amfani dukka sun ƙone ƙurmus, kuma ba a san dalilin tashin wutar ba.
Shugaban ƴan gudun hijira na jihar Bauchi Alhaji Buba Musa Shehu ya roƙi gwamnatin jihar Bauchi da Borno da Yobe da Kuma hukumar raya shiyyar arewa maso gabas NEDC, su agaza wa mutanen da suka gamu da ibtilain gobarar don komai nasu ya kone.
The Stentor News
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V