Dawowa Da Sanusi II Sarki Ba Zai Haifawa Kano Da Mai Ido Ba – Wata Kungiya Ga Majalisa

IMG 20240207 115010

Wata kungiya mai suna Society For Peace Development and Education” ta bukaci majalisar dokokin jihar kano ta yi watsi da kiran da wata kungiya ta yi na rushe sabbin masarautun jihar kano tare da dawo da Muhammad Sanusi kan sarautar masarauta Kano.

Idan za’a iya tunuwa a ranar talata cewa, wata kungiya mai suna kungiyar yan dangwale ta jihar kano ta bukaci majalisar dokokin jihar kano data rushe sabbin masarautun Gaya, Rano, Bichi da karaye tare da dawo da tsohon Sarkin Kano Muhammad Sanusi kan karagar mulkin Kano.

Hakan na kunshe ne cikin wata wasikar koke da kungiyar ta rubuta majalisar dokokin jihar kano a ranar Alhamis kuma ta karba ta hanyar Sanya hatimin majalisar.

Wasikar ta ce Kiran da waccan kungiya ke yi na rushe sabbin masarautun da dawo da Sanusi akwai siyasa a Cikin, don haka ta roki majalisar da tayi watsi da kiran.

” Sabbin masarautun jihar kano ba kirkirarsu akai ba, domin sun kasance tun kafin zuwa turawa Nigeria, kawai an farfado da martabar su ne, don cigaban al’umma yankunan”.

” Tun bayan farfado da martabar wadannan masarautun an sami cigaba ta fuskar Ilimi, Lafiya, da Ababen more rayuwa, da samar da aiyukan yi ga matasa da sauran al’umma, hakan tasa al’ummar yankunan Bichi, Gaya, Rano da Karaye suke kaunar masarautun su kan cigaban da suka samu”. Inji Wasikar.

Kungiyar mai dauke da sa hannun Sakataren kungiyar Sociaty for peace development and Education Murtala Musa Lisa, ta ce game da dawo da Muhammad Sanusi kan karagar mulkin Kano hakan ba abun da zai haifar illa rashin zaman lafiya a jihar kano baki daya.

” Kowa ya san abun da ya faru na tashin hankali da aka samu lokacin da aka nada Sanusi a Matsayin Sarkin Kano, don haka muke gani sake dawo da shi zai iya haifar da rashin zaman lafiya a jihar Kano baki daya”.

” Kuma ba haka kawai aka cire shi sai da aka same shi da laifuka daban-daban kuma aka ja kunnensa a hakan, kamar yadda akai masa lokacin da yake jagorantar Babban Bankin Nigeria”. A cewar Wasikar

Kungiyar ta ce ” ita waccen kungiya da ta ce a cire Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a dawo da Sanusi to da wanne laifi za’a yi amfani wajen cire shi, tun da dai kowa ya sani sarkin baya sanya kansa cikin duk wani ruɗani sabanin yadda Sanusi ya rika yi. In Ji wasikar

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *