Yan Sanda Sun Kama Shugabar Mata Masu Gurasa Da Suka Yi Zanga-Zanga A Kano

FB IMG 1707052631947

Jami’an rundunar ‘yan sanda sun kama Fatima Auwal, shugabar matan da jagoranci masu gurasar da suka gudanar da zanga-zangar lumana , a Kano a makon daga gabata.

Alfijir labarai ta rawaito Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen Jakara ce ta kama shugabar a ranar Asabar.

Zanga-zangar da masu yin Gurasar suka yi a Kano ranar Alhamis sun yi ne kan tsadar farashin fulawa.

Rahotanni sun nuna cewa an kama Fatima Auwal ne biyo bayan korafe-korafen da ‘yan sanda suka samu daga wasu mata biyu da wani mutum da suka ce ita ba ‘yar kungiyarsu ba ce, don haka ba ta da hurumin yin amfani da sunan su har ta jagoranci zanga-zanga .

Sai dai daga baya an sake ta a matsayin beli da yamma bayan wasu sun shiga maganar, ta kuma bukaci ta dawo ofishin ‘yan sanda a yau Lahadi.

Da take zantawa da SOLACEBASE kan lamarin, Fatima Auwal, ta ce ta yi mamakin tambayar da ‘yan sanda suka yi mata kan zanga-zangar lumana da ta yi da nufin fadawa gwamnati mawuyacin hali da suka shiga sakamakon tashin farashin fulawa.

” ‘Yan sandan sun ce wasu mata da wani mutum ne suka yi korafin cewa mun yi amfani da sunan kungiyarsu yayin zanga-zangar wanda hakan ba gaskiya ba ne”. A cewar Fatima Auwal

‘’Mutanen da suka shigar da korafin su ne masu sayar da gurasa ne, alhali mu kuma mu ne masu hada gurasar. Don haka ya ba ni mamaki cewa sana’ar da mutane da yawa suka san mu akai za’a ce munyi sojan gona akan ta.’’

‘’Eh ‘yan sanda sun nemi da in dawo ofishina yau bayan an sake ni a matsayin beli jiya da daddare.

Da yake mayar da martani kan wannan al’amari, Shugaban kungiyar Jakara Junction Gurasa Bakers, Multi-Purpose Cooperative Society, Hadiyyatulahi Hamisu ya tabbatar da cewa su ne suka shigar da korafin a wajen ‘yan sanda kan amfani da sunan kungiyarsu da masu zanga-zangar suka yi.

Ko da yake Hamisu ya ce shugabar zanga-zangar, Fatima Auwal ita ma mai yin Gurasa ce kuma ita ce shugabar karamar kungiyar masu gurasa.

”Shi ya sa muka kai karar ‘yan sanda.”

”Abin da muke nema a gare ta shi ne ta koma kafafen yada labarai ta janye maganarta.”

Hadiyyatulahi wanda shi ma ya tabbatar da hauhawar farashin na fulawa, ya ce kalubalen tattalin arziki ne na yau da kullum da ake fuskanta a ko ina.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *