Daga Baba Usman Gama
Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya bukaci shugaba Tinubu da ya rufe idonsa ya dauki kwararan matakai kan mukarrabansa da suka kasa gudanar da ayyukan da ke wuyayensu.
INEC za ta gudanar da zaɓukan raba gardama da kuma na cike gurbi na kujerun majalisun tarayya da kuma na jihohi a faɗin jihohi 26 a yau Asabar.
Gwamnati ta danganta ƙara taɓarɓarwar wutar lantarki a ƙasar nan da dalilan rashin samun wadataccen gas ga kamfanonin samar da wuta wato, GenCos.
Gwamnatin jihar Oyo ta rufe coci saboda damun maƙwabta da hayaniya.
Olayemi Cardoso ya amince an saki $500m domin biyan bashin kudin waje da ake bin CBN a Najeriya.
Rundunonin ‘yan sanda sun ce za su takaita zirga zirga a wasu yankuna a yayin da INEC ke gudanar da zabukan cike gurbi a jihohi 26 na Nijeriya ranar Asabar.
Atiku Abubakr yace Kuskure ne shugaba Tinubu ya ce CBN ya karbe kudaden cinikin da NNPC ke yi
Manoma dubu 36 za su ci gajiyar shirin noman Fadama na GO-CARES a Gombe.
Sanata Elisha Abbo ya zargi shugabar kotun daukaka kara, Monica Dongban-Mensen da karbar cin hanci.
‘Yan bindiga sun sace mata kusan 55 yan raka amarya har ɗakin aurenta a titin zuwa Damari, karamar hukumar Sabuwa a Katsina.
Kotun majalisar dinkin duniya ta ce tana da hurumin sauraron shari’ar Ukrane da Rasha.
AFCON: Nigeria ta tsallaka semi final bayan samun nasara akan Angola da ci 1:0 a wasan jiya.
AFCON: Congo ta tsallaka semi final bayan samun nasara akan Guinea da ci 3:1 a wasan jiya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V