Wannan matashi dan Adaidaita sahu ya kara fito da darajar musulmai a idon duniya:
Alfijir labarai ta rawaito wani dan jihar Katsina dake tuka babur din adaidaita Sahu ya mayar wa wata mata yar ƙabila wayar sama da N1m da ta manta cikin babur din.
Wata mata yar kabilar Igbo ce, ta hau Adaidaitan wajen sauka ta mance da wayarta kirar Iphone 13 Pro Max
An kiyasta kudin irin wannan wayar a wannan lokacin, Inda kudinta sun haura naira miliyan ɗaya a yanzu.
Abin farin ciki da jin daɗi matashin ya nemi matar sannan ya kawo mata wayar har inda take, ta kuma yi niyyar bashi tukuici ya ce, ba ya buƙata domin hakkinta ne, ta manta a cikin babur din, shi kuma haƙƙinsa ne ya nemo duk wanda ya manta wani abu a cikin abin hawansa ya damka masa kayansa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V