An ba su shaguna a Sabuwar Kasuwar Zamani da ke Damaturu da kuma tallafin kudi N100m
Alfijir labarai ta rawaito Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayar da gudunmuwar N100m ga wadanda gobara ta yi wa barna a Kasuwar Wayoyi da ke Damaturu.
A yayin ziyarar da ya kai wurin da gobarar ta tashi domin jajanta wa wadanda abin ya shafa, gwamnan ya bayyana ta a matsayin abin takaici da kuma babbar asara ga ’yan kasuwar da lamarin ya shafa da kuma jihar baki daya.
“Abin takaici ne yadda wannan bala’i ke faruwa a yanzu yayin da matasanmu ke kokarin gina sana’o’insu,” in ji shi, kamar yadda kakakinsa, Mamman Mohammed, ya sanar.
Sanarwar ta kara da cewa, “Gwamnati za ta ci gaba da taimaka muku wajen dawowa kan sana’o’inku, domin samar da karin ayyukan yi ga matasan mu.”
Ya kuma umurci sakataren gwamnatin jihar da ya raba shaguna ga wadanda abin ya shafa a sabuwar kasuwar zamani ta Ibrahim Gaidam da aka gina a Damaturu.
Ya kara umartar ma’aikatar gidaje ta jihar da ta tantance irin barnar da aka yi, da nufin sake gina shagunan da abin ya shafa ga masu su.
Buni ya kuma yi kira ga jama’a da su yi taka-tsantsan tare da daukar matakan da suka dace kan abubuwan da za su iya haddasa tashin gobara a gida da wuraren kasuwancinsu.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V