A halin yanzu dai shugaba Bola Tinubu na fuskantar matsin lamba kan zargin da ake yi wa shugaban ma’aikatan fadar gwamnatinsa wato, Femi Gbajabiamila kan cin hanci da rashawa.
Alfijir labarai ta rawaito a ranar Litinin cewa Gbajabiamila ya na daya daga cikin wadanda suka tafka mummunan cin hanci da rashawa da aka bankado karkashin Ahmed Kuru, babban jami’in hukumar kula da kadarorin Najeriya (AMCON) da kuma tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Godwin. Emefiele.
Babban mai bincike na musamman, Jim Obazee, a rahoton da ya fallasa, ya bayyana yadda Gbajabiamila ya fito a badakalar yace, “manyan kadarorin Ikoyi Ahmed Kuru, Femi yana daga cikin wadanda suka amfana a zamaninsa na Shugaban Majalisar Wakilai,” a cewar manyan majiyoyi a fadar shugaban kasa.
Daya daga cikin majiyar ta bayyana cewa Gbajabiamila yayi ruwa yayi madaukiya domin ya tabbatar da cewa Kuru ya ci gaba da zama shugaban AMCON bayan wa’adin sa ya kare da tsawon shekaru.
Tuni dai wasu sabbin bayanai suka fito kan yadda Godwin Emefiele da Ahmed Kuru, shugaban AMCON suka hada baki wajen cin zarafi da cin hanci da rashawa wajen mallakar bankunan da suke so ta hanyar amfani da kudaden jama’a wajen damfara ta kwace bankunan Polaris, Keystone da Unions Banks.
SaharaReporters ta samu rahoton mai bincike na musamman kan binciken Emefiele wanda ya bankado makudan kudaden al’umma da suka yi sama dasu bankunan da Emefiele da AMCON suka yi a karkashin shugabancin Kuru.
SaharaReporters a ranar 10 ga watan Janairu ta ruwaito cewa babban bankin Najeriya CBN ya rusa bankin Titan Trust, Union Bank, Polaris Bank da Keystone Bank.
Hakan ya biyo bayan rahoton da babban mai bincike na musamman kan babban bankin Najeriya Jim Obazee bayan ya mika wa shugaba Bola Tinubu.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V