Takaitattun Labaran Duniya Na Safiyar Lahadi 09/07/1445AH – 21/01/2024

best seller i2

Daya Baba Usman Gama

Rundunar ‘yan sanda sun tabbatar da kubutar da ‘yan matan nan 5 da ke hannun masu garkuwa da mutane bayan ‘yan bindiga sun kashe ‘yar’uwarsu wato Nabeeha Al-Kadriyar.

Rundunar ‘yan sanda ta ce dakarunta sunyi nasarar kama wasu masu aikata laifuka su 13 a Abuja, ciki har da gawurtattun masu garkuwa da mutane.

Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, da wasu sanatoci sun tarbi dan takarar gwamna na jam’iyyar YPP a jihar Akwa Ibom, Bassey Albert zuwa APC.

Gidauniyar MacArthur za ta bai wa Jami’ar Ahmadu Bello gudunmuwar dala miliyan 15 domin bunkasa harkokin karatu da bincike.

Magidanci ya yi kukan kura, ya kashe ɗan bindiga yayin ƙoƙarin hana garkuwa iyalin sa a jihar Taraba.

Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta kaddamar da wani shiri na tallafawa mata masu haihuwan ‘yan biyu da ‘yan uku.

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya amince da biyan ma’aikata naira dubu 35 don rage musu radadin cire tallafi.

An rantsar da Felix Tshisekedi a matsayin sabon shugaban Jamhuriyar kongo a wa’adi na biyu.

Yara ɗalibai 13 sun mutu sakamakon tashin gobara a ɗakin kwanansu a kasar China.

Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, da wasu sanatoci sun tarbi dan takarar gwamna na jam’iyyar YPP a jihar Akwa Ibom, Bassey Albert zuwa APC.

Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta kaddamar da wani shiri na tallafawa mata masu haihuwan ‘yan biyu da ‘yan uku.

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya amince da biyan ma’aikata naira dubu 35 don rage musu radadin cire tallafi.

An rantsar da Felix Tshisekedi a matsayin sabon shugaban Jamhuriyar kongo a wa’adi na biyu.

Yara ɗalibai 13 sun mutu sakamakon tashin gobara a ɗakin kwanansu a kasar China.

An sallami kocin Senegal daga Asibitin Ivory Coast bayan kwantar da shi.

Kocin Kamaru Song ya dauki alhakin rashin nasarar Kamaru a karawar su da Senegal.

AFCON: Angola ta sami nasara akan Mauritania da ci 3:2 a wasan jiya.

AFCON: Algeria da Tunisia sun tashi 1:1 a wasan jiya.

EPL: Brentford ta sami nasara akan Nottm Forest da ci 3:2 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *