Iftila’in Mummunar Gobara Ta Hallaka Magidanci Da Matarsa Yayansa Biyar A Kano

FB IMG 1705326964711

Muneer Ibn Ibrahim shi ne mai gidan hayar da suke, ya sheda cewa, wani firinji ne yai sanadin tashin gobarar bayan ya kama da wuta

Alfijir labarai ta rawaito wani magidanci mai suna Shu’aibu Ahmad mazaunin unguwar Tudun Wada Brigate a karamar hukumar Nassarawa a birnin Kano, ya rasa ransa tare da matar Binta da ‘yayansu guda 5.

Hakan ya faru ne sakamakon tashin wata mummunar gobara da ta afku sabadiyar kawo wutar lantarki mai karfin gaske da misalin karfe 12 na daren Lahadin da ta Gabata.

Muneer Ibn Ibrahim shi ne mai gidan hayar da suke, ya sheda cewa, wani firinji ne yai sanadin tashin gobarar bayan ya kama da wuta a lokacin da aka kawo wutar, shi kuma marigayin da iyalansa suna bacci ษ—akin nasu kuma a rufe.

Wannan dalilin ya jawo hayaki ya turnike su inda hakan yai sanadiyar mutuwarsu su bakwai lokaci daya.

An yi jana’izarsu Kamar ya ddaaddini ya tanadar.

Allah ya jikansu da rahama Allah ya kyautata makwancinsu.

Ibtila i
Ibtila i

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai ๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *