Daga Baba Usman Gama
Madugun Jam’iyyar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce jita-jita ce batun da ake yadawa cewa yarjejeniya suka yi da Shugaba Tinubu aka dawo musu da kujerar Gwamnan Kano.
Sojoji sun kashe kwamandojin ISWAP uku a Borno.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce yana cikin murna da farin ciki tare da al’ummar jihar Kano da duka masoyansa na Najeriya da ma duniya baki ɗaya bisa nasrar da ya samu a kotun ƙolin ƙasar.
INEC tace jimillar ‘yan Nijeriya 4,567,689 za su yi zabe a zaben cike gurbi da zai gudana a watan Fabrairun a jihohi 27.
Dangote ya gode wa Tinubu kan ƙwarin gwiwar da ya samu na fara aiki matatarsa.
Gwamnatin jihar Yobe ta biya N708m haƙƙoƙin tsoffin ma’aikata 461.
Wata kotun majistare a Jihar Legas ta ba da umarnin tsare wani mutum a gidan yari na Kirikiri kan yin lalata wata yarinya ‘yar shekara 14.
Hisbah ta kama mota maƙare da kwalaben barasa dubu 24 a Kano.
’Yan bindiga sun kashe shugaban kauyen Wuro Musa dake Karamar Hukumar Yorro dake jihar Taraba, Jauro Kabiru Gambo.
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina ta kama wani mutum da dauke da buhu 45 na miyagun kwayoyi da sauran kan maye.
Rundunar ‘yan sandan Jihar Ogun ta tabbatar da kisan basaraken masarautar Shagamu a Jihar Ogun, Cif Bashorun Abiodun.
Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ya yi barazanar daina tallafa wa kungiyar kwallon kafar Gombe United saboda rashin katabus.
Jirgin sama dauke da mutane 378 ya kone a Japan.
William Lai ya lashe zaɓen shugaba ƙasar Taiwan.
Harin sama ya kashe sama da mutane 30 a Sudan.
Ministan harkokin Iran ya goyi bayan Houthi kan hare-haren da suke kai wa.
Dan wasan Manchester City Haaland zai iya jinya zuwa ƙarshen watan Janairu, kamar yadda kocin ƙungiyar Pep Guardiola ya bayyana.
Burnley ta ɗauki Fofana aro daga Chelsea.
EPL: Chelsea ta sami nasara akan Fulham da ci 1:0 a wasan yau.
Laliga: Las Palmas ta sami nasara akan Villarreal da ci 3:0 a wasan yau.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl