Takaitattun Labaran Duniya Na Yammacin Juma’a 12/01/2024CE – 30/06/1445AH

IMG 20240103 WA0021

Daga Baba Usman Gama

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce ya yi farin ciki maras misaltuwa da hukuncin kotun ƙolin da ya tabbatar da nasararsa a matsayin halastaccen gwamnan Kano Kuma yana godiya ga al’ummar jihar bisa addu’o’in da suka yi masa.

Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Dare na Zamfara a jawabin gwamnan ya yi kira ga jam’iyyar adawa da ta zo a haɗa kai wajen ceto jihar daga halin da take ciki.

Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar Gwamna Bala Mohammed na Bauchi.

Kotun Ƙoli ta tabbatar da Babajide Sanwo-Olu a matsayin halastaccen gwamnan jihar Legas.

Kotun ƙoli ta tabbatar da zaɓen Francis Nwifuru na APC a matsayin gwamnan jihar Ebonyi.

Gwamna Caleb Mutfwang na jami’yyar PDP a matsayin halastaccen gwamnan jihar Filato.

Wasu ‘yan bindiga kimanin su 40 sun yi awon gaba da mutane 23 yayin wani hari da suka kai kauyen Kawu da ke Karamar Hukumar Bwari a Abuja.

Jam’iyyar APC a Kano sun ce sun rungumi ƙaddara game da hukuncin kotunƙoli da ta tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf na NNPP.

Isra’ila ta ce Afirka ta Kudu ta jirkita gaskiya a zargin kisan ƙare-dangi.

An rage lokutan ibada a Zambiya don daƙile yaɗuwar kwalara.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ayyana Cabo Verde a matsayin ƙasar da ta rabu da zazzabin cizon sauro.

An tsare tsohon ministan Kenya a Uganda kan zargin safarar zinare.

Burundi ta kulle iyakarta da Rwanda kan zargin Kigali da goyon bayan ‘yan tawaye.

Sojin Somalia sun fara kokarin kwato jirgin MDD da Al Shabab ta kwace.

Yemen ta yi alkawarin mayar da martani biyo bayan harin Amurka da Birtaniya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *