Badakala! Tsohuwar Ministar Jin Kai Sadiya Farouq Ta Mika Kanta Ofishin EFCC

IMG 20240108 122945

Bisa radin kaina, na isa hedikwatar hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zango kasa (EFCC)

Alfijir labarai ta rawaito tsohuwar ministar ayyuka da jin kai ta Nijeriya Sadiya Umar Farouq ta kai kanta a gaban hukumar EFCC a Abuja babban birnin Nijeriya.

Ana zargin wani dan kwangila a ma’aikatarta da almundahanar sama da naira biliyan 37.

Tun a makon da ya gabata ne hukumar ta gayyaci tsohuwar ministar ta gabatar da kanta, sai dai wasu majiyoyi sun tabbatar da ba ta je ba.

A safiyar Litinin tsohuwar ministar ta fitar da sanarwa a shafinta na X inda ta sanar da zuwanta hukumar.

“Bisa radin kaina, na isa hedikwatar hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zango kasa (EFCC) domin karbar goron gayyata domin karin haske dangane da wasu lamura wadanda hukumar ke bincike a kai,”

Sai dai a kwanakin baya, tsohuwar ministar ta wallafa wani sako a ranar 26 ga watan Disambar 2023 inda take nesanta kanta daga duk wasu rahotanni da ke nuna cewa EFCC na bincike a kanta inda hasalima ta yi zargin ana kokarin bata mata suna.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *