Zargin Badakala! Shugaba Tinubu Ya Bada Umarnin A Binciki Ministar Jin-Kai, Betta Edu

FB IMG 1704701650847

Kungiyoyin sun bukaci Tinubu ya sauke Betta Edu daga mukaminta don samun damar gudanar da ingantaccen bincike ba tare da samun wani katsalandan ba.

Alfijir labarai ta rawaito Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan badakalar Naira miliyan 585.189 da ake zargin ministar jin-kai, Beta Edu.

Wannan na zuwa ne bayan wasu kungiyoyi da sauran jama’a suka rika matsa wa Tinubu lamba kan a gudanar da bincike a,tare duma hukunta ministar matukar aka same ta da laifi.

Kungiyoyin sun bukaci Tinubu ya sauke Betta Edu daga mukaminta don samun damar gudanar da ingantaccen bincike ba tare da samun wani katsalandan ba.

Tun da farko an zargi Betta Edu ne da rubuta wa Akanta-Janar ta Najeriya wata wasika da ke bukatar ta sanya wadannan kudade a cikin asusun wata mata da ba a san kowace ce ba, lamarin da ya tayar da kura.

Sai dai jim kadan bayan fitar labarin, Akanta-Janar din ta ce ba ta saki wadannan kudaden ba, saboda doka sam ba ta ba ta damar sanya kudade a asusun wani mutum ba.

Ya zuwa yanzu dai ofishin ministar ya ce ta umarci a biya wadannan kudade ne don bai wa marasa galihu a Jihohin Akwa Ibom, Legas, Kuros Ribas da Ogun a matsayin tallafi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *