Wani masoyin Tsohon Shugaban ‘Kasa Buhari sun gamu a karon Farko tare da bashi kyautar Mota.
Alfijir labarai ta rawaito a ranar Asabar da ta gabata ne wani Dattijo masoyin tsohon Shugaban Kasar ya samu damar ziyartar tsohon shugaban kasar General Muhammadu Buhari, a gidansa dake Daura.
Ziyarar ta samo asali ne domin zuwa da nuna masa wani cikakken masoyinsa na garin Yashe, wanda aka fi sani da suna sai BABA BUHARI Ko Kuma HARUNANMU.
Hakika Tsohon Shugaban Kasa yaji dadi da nuna farin cikinsa akan wannan masoyin nasa, domin yaji duk irin soyayyar da yake masa da kuma hidima da yake akansa.
Tsohon Shugaban Kasa Ya Gwangwaje Dattijon Da Sabuwar Mota kirar GOLF 3, Da Kuma Buhun Shinkafa 5, Da Kuma Wasu Kudade.

Buhari Sallau
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai ๐๐
https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl