Ibtila I! Wani Hatsarin Ya Rutsa Da Tawagar Mataimakin Gwamnan Sokoto Wasu Sun Rasa Rayukansu

IMG 20240104 001605

A yammacin ranar Laraba ne wani mummunan hatsari ya afku a jihar Sokoto wanda ya rutsa da ayarin mataimakin gwamna Idris Gobir, wanda yayi sanadin asarar rayuka biyu.

Alfijir labarai ta rawaito wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa yace, wata motar ‘yan sanda da ke cikin ayarin motocin dauke da jami’an yan sanda da mai daukar hoto Buhari Tanko ta yi hatsarin.

Majiyar ta tabbatar da cewa jami’an ‘yan sandan da ba a tantance ko su waye ba da kuma mai daukar hoto Tanko sun rasa rayukansu a wurin.

Da yake bayyana alhinin lamarin, majiyar ta ce, “Na tabbatar da cewa motar da ta yi hatsarin motar ‘yan sanda ce, inda mai daukar hoton na tare da su a cikin mota lokacin da lamarin ya faru. Abin takaici ne kuma abin bakin ciki ne.”

A halin da ake ciki, Gwamna Ahmed Sokoto, tare da mataimakin gwamnan, ya jagoranci wata tawaga zuwa Sabon Birni domin gudanar da ayyuka.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Ahmed Rufa’i, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da wata mota a cikin ayarin mataimakin gwamnan.

kuma an tabbatar da mutuwar direban motar, jami’in ‘yan sanda, tare da mutum daya, mai daukar hoto a cikin ayarin.

Mutanen da suka samu raunuka a hatsarin na ci gaba da karbar magani a asibitin koyarwa na Jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *