An mayar da yaran da aka sato a Bauchi don sayarwa a Kano hannun iyayensu

FB IMG 1703934479715

Gwamna An Kano bba Kabir Yusuf  yamil haɗa wasu iyaye da yaransu da aka sace.

Alfijir labarai ta rawaito hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren watsa labaru ga gwamnan, Sanusi Bature ya fitar.

Gwamna Abba Kabir ya nuna farin cikinsa lokacin da yake bai wa iyayen ƴaƴansu, inda ya kuma yaba wa rundunar ƴan sandan jihar ta Kano bisa namijin ƙoƙari da suka yi wajen kuɓutar da yaran.

An miƙa shida daga cikin yaran bakwai da aka ceto ga iyayensu waɗanda ƴan asalin jihar Bauchi bayan nasarar da ƴan sandan Kano suka yi wajen kama mutanen da suka sace su.

Gwamnan ya buƙaci iyayen yaran da su rika sa ido kan ƴaƴansu domin tabbatar da halin da suke ciki a kowane lokaci.

FB IMG 1703934393018
📸SP Kiyawa

Ya kuma yi kira ga takwaransa na Bauchi, Bala Mohammed, da ya ɗauki tsassauran mataki ga dukkan waɗanda aka kama da laifin satar yara.

A martaninsu, iyayen yaran sun nuna godiya ga gwamnan Kano da kwamishinan ƴan sandan jihar kan ceto ƴaƴan nasu.

A ranar Alhamis, rundunar ƴan sandan jihar Kano ta yi nasarar kama wani gungun mutanen da suka ƙware wajen satar yara da kuma safararsu zuwa waɗansu jihohi a kudancin Najeriya.

Ƴan sanda sun ce an cafke mutanen ne a tsakanin jihohin Kano da Bauchi da Anambra da Imo da kuma Legas

FB IMG 1703934465751
📸SP Kiyawa

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl


Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *