Wasu fursunoni uku sun tsere daga gidan yarin Ijebu Ode da ke jihar Ogun a kudancin Najeriya.
Alfijir labarai ta rawaito Hukumomin gidan yarin sun tabbatar da tserewar fursunonin guda uku
Sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kula da gidajen gyara hali reshen jihar Ogun Victor Oyeleke ya fitar, ta ce fursunonin sun tsere ne ranar Asabar da tsakar dare.
Fursunonin sun tsere ne ta hanyar tsallaka katanga.
A cewar sanarwar, tuni aka shiga farautar fursunonin – hukumomin sun ce suna da bayanansu da kuma iyalansu, suna kuma aiki da sauran hukumomi domin dawo da su cikin gaggawa.
Har ila yau, sanarwar ta ce ɗaya daga cikin fursunonin da suka tsere yana zaman gidan yarin ne kan hukuncin fashi da makami da aka yanke masa, ɗayan kuma an ɗaure shi a gidan yarin ne kan aikata kisa.
Na ukun kuma yana zaman gidan yari kan aikata cin zarafi ta hanyar lalata.
Tserewar furusnoni ko fasa gidajen yari ba sabon abu ba ne a Najeriya.
Masana kuma na bayyana damuwa kan haɗarin da ke tattare da matsalar fasa gidajen yari wanda ke bayyana irin rikon sakainar kashi da ake yi wa gidajen yarin musamman a halin rashin tsaro da dukkan sassan ƙasar ke fuskanta.
BBC
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp
