Takaitattun labaran Duniya Na Yammacin Asabar 09/06/1445AH – 23/12/2023

best seller i

Daga Baba Usman Gama

Tsohon Gwamnan CBN Emefiele, ya koma gida bayan ya cika sharuɗɗan belin da kotu ta ba shi.

Sheikh Dahiru Bauchi ya nemi kotu ta yi adalci a shari’ar zaɓen Kano.

Sojojin Najeriya sun kuɓutar da mutum 52 da aka yi garkuwa da su a Sokoto.

Wasu ƴan bindiga sun kashe wani Dokta David Adefikayo, shugaban asibitin Dafikayo a gidansa da ke Kanbi a ƙaramar hukumar Moro a jihar Kwara.

Fitaccen jarumi a masana’antar shirya fina-finai ta kudancin Najeriya, Nollywood, Dejumo Lewis, ya mutu yana da shekara 80 a duniya.

CBN ya cire haramcin amfani da kuɗin crypto a bankunan Najeriya.

Jarumar fina-finan ‘Nollywood’, Mercy Aigbe ta tsallake rijiya a wani mummunan hatsarin mota a kan hanyarta ta zuwa Legas.

Ana makokin mutum 14 da ɗan bindiga ya kashe a Jami’ar Prague a jamhuriyyar Check.

Abincin bikin Kirsimeti ya sa ma’aikatan kamfanin jirgin sama amai da gudawa

Sama da ma’aikatan kamfanin jirgin sama 700 suka kamu da amai da gudawa sakamakon cin abincin kirsimeti a Faransa.

An kammala shara’ar aikata laifin kisan kiyashin ga wasu yan kasar Rwanda biyu a Belgium.

Rashin jituwa na kara yin karfi tsakanin Mali da Algeria kan ‘yan aware.

Mutane 12 ne suka jikkata a cikin wani harin jirgi marar matukin kasar Ukraine kan Donetsk.

EPL: West Ham ta sami nasara akan Manchester United da ci 2:0 a wasan yau.

EPL: Luton ta sami nasara akan Newcastle da ci 1:0 a wasan yau.

EPL: Tottenham ta sami nasara akan Everton da ci 2:1 a wasan yau.

Laliga:Atlentico Madrid ta sami nasara akan Sevilla da ci 1:0 a wasan yau.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *