Takaitattun Labaran Duniya Na Yammacin Juma’a 08/06/1445 – 22/12/2023CE

best seller i

Daga Baba Usman Gama

Shugaba Tinubu ya isa Jihar Legas inda zai yi hutun karshen shekara.

Shugaba Tinubu ya ba da umarnin biyan masu cin gajiyar NPower mutun dubu Dari 4.

An gano asusun banki 593 da Emefiele ya boye kudade a kasashen waje.

An kafa kwamatocin yaƙar satar ɗanyen mai da inganta tattalin arzikin Najeriya.

Kotun ƙoli ta tabbatar da zaɓen gwamna Peter Mbah na Enugu.

Ƴan sanda a Kano na neman ƴan daba 72 ruwa-a-jallo.

Sule Lamido ya ce a kan menene za a bari Bola Tinubu yana yi wa ‘yan jam’iyyar PDP shisshigi a siyasar Ribas.

Gwamnatin jihar Kano ta ware Naira Biliyan 15.97 don yin wasu manyan ayyuka 2 a Kwaryar birni.

Yan Sanda sun gurfanar da wani mutum da Ya Kashe Mahaifinsa a Kwara.

Wasu mata 2 da Karamin yaro sun makale yayin da gini mai Hawa 2 ya rufta kansu a Jihar Legas.

‘Yan bindiga sun kashe akalla mutum 20 a wani kauye na Jumhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Ƴan sanda na binciken ɗan bindigar da ya kashe mutum 14 a Czech.

Rukunin karshe na dakarun Faransa sun kammala ficewa daga Nijar.

Yakin Sudan ya raba mutane miliyan 7 da muhallansu.

Sojojin Amurka sun kashe jagoran kungiyar Al-Shabab a Somaliya.

Turkiyya ta kama sama da mutum 300 bisa zargin ta’addanci.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *