Labari Mai Dadi! Wani Gwamnan Ya Saka Amince Da Kyautar Naira 100,000 Ga Ma’aikatan Jihar

ALFIJIR 1

Gwamna Francis Nwifuru a ranar Alhamis ya bayyana amincewa da kyautar N100,000 na Kirsimeti ga ma’aikatan gwamnati a jihar Ebonyi.

Alfijir labarai ta rawaito Nwifuru ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da masu ruwa da tsaki da kuma dattawan jihar a yayin bikin kaddamar da shirin dabbobi na uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, wanda ya gudana a cibiyar ecumenical dake Abakaliki.

Gwamnan ya jaddada cewa arzikin jihar na al’umma ne kuma a sakamakon haka ba za a bar su su ci gaba da fama da talauci ba.

Ya ce, “Na yanke shawarar daukar mataki mai kyau, abu ne mai wahala amma dole ne mu yi hakan. Dole ne ma’aikatan wannan jiha su rayu kamar sauran a wannan lokacin Kirsimeti. A wannan kakar kana bukatar ka albarkaci maƙwabcinka, kana buƙatar zama mai albarka ga gidanka.

“Kuma a matsayinsa na shugaban jihar, ya zama dole ya zama mai albarka a gidajen kowa da kowa a jihar nan. Ba zan iya cewa ina yin haka ba saboda ba kudina ba ne, kudin jihar ne nake amfani da su, wanda aka zabe ni in sarrafa.

“Kuma na yanke shawara da ’yan kwamitin da manyan jami’an gwamnati, tun da na shigo, cewa ma’aikata a Jihar Ebonyi su sami abin murna.

“Zan yi ganawa da shugabannin kananan hukumomi, kuma kowane ma’aikaci a jihar nan dole ne ya sami N100,000 a matsayin kyautar Kirsimeti, ciki har da buhun shinkafa.”

Ku tuna cewa Gwamna Siminialaye Fubara na Jihar Ribas ne ya fara amincewa da irin wannan adadin ga ma’aikatan gwamnati a wannan kakar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *