Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Ya Tura Sunayen Mutum 11, Wanda Yake So Majalisar Dattawan Najeriya Ta Sahale Masa Ya Nada su A Matsayin Sabbin Alkalan Kotun Koli.
Alfijir labarai ta rawaito Tinubu ya Turawa Majalisar Sunayen Ne Domin Ta Tantance Su Kana ta Amince Dasu, Bayan Zabosu da hukumar kula da sharia ta kasa NJC Tayi.
A Sanarwar Da Daraktan Yada Labaran Kotun Koli Soji Oye ya Fitar Yace An Amince Da Nadin Alkalan ne a Yayin Taron Hukumar Kula da Shari’a Karo na 104,Wanda Ya Gudana a Abuja.
Kundin Tsarin Mulkin Najeriya Dai Ya Sahale A Nada Alkalai 21 ne A Kotun Koli.
Jerin Sunayen Da Shugaba Tinubu Ya Turawa Majalisar Sun Hadar da
(1) Hon. Justice Jummai Hannatu Sankey, OFR
(2) Hon. Justice Chidiebere Nwaoma Uwa
(3) Hon. Justice Chioma Egondu Nwosu-Iheme
(4) Hon. Justice Haruna Simon Tsammani
(5) Hon. Justice Moore Aseimo A. Adumein
(6) Hon. Justice Obande Festus Ogbuinya
(7) Hon. Justice Stephen Jonah Adah
(8) Hon. Justice Habeeb Adewale O. Abiru
(9) Hon. Justice Jamilu Yammama Tukur
(10) Hon. Justice Abubakar Sadiq Umar
(11) Hon. Justice Mohammed Baba Idris
Alkalan da Aka Tura Sunayen Nasu Zasu Shafe Shekaru 4 ne a Matsayin Alkalan Kotun Kotu, Matukar Majalisar Ta Amince Dasu.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp