Takaitattun Labaran Duniya Na Safiyar Talata 19/12/2023 – 07/06/1445AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Shugaba Tinubu ya karbi bakuncin shugaban kamfanin Total Energies, Mista Patrick Pouyanne, a fadarsa da ke Abuja.

INEC tace za’a gudanar da zaɓukan cike gurbi a fading kasa watan Fabarairu.

Wike da Fubara sun sasanta rikicin jihar Rivers bayan ganawa da Tinubu.

An garzaya asibiti da Hudu Ari Kwamishinan Zaben Adamawa, bayan ya yanke jiki ya fadi ana tsaka da shirin zuwa gurfanar da shi a kotun jihar.

Sojoji sun ceto mutum 13 da ’yan bindiga suka sace a yankin Mutunji sannan suka kama wasu mutane 11 dauke da makamai a Jihar Zamfara.

Babbar Kotun Tarayya ta sake rufe asusun bankunan gwamnatin jihar Oyo.

Babban kotun tarayya mai zama a garin Abuja ta haramtawa tsohuwar minista Pauline Tallen rike wani mukami na gwamnati a kasar nan.

Gwamnan jihar Neja, Umar Bago, ya haramtawa ma’aikatan gwamnati sanya tufafin gargajiya zuwa ofis a jihar.

Mazauna garin Tsohuwar Kuyello a yankin Birnin Gwari na barin gidajensu a sakamakon rikicin ’yan ƙungiyar Ansaru da barayin daji a yankin.

’Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane 11 a kauyen Kubuwo da ke Karamar Hukumar Kagarko a Jihar Kaduna, inda suka bukaci Naira miliyan 16 da sabbin babura hudu a matsayin fansa.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau Jibrin na kokarin shawo kan Shoprite domin canja shawarar barin jihar Kano.

Mazauna birnin Wad Madani na ƙasar Sudan sun ce dakarun RSF sun kai hari a wani asibiti tare da ƙwace wani sansanin sojoji.

Kwamatin Tsaro na MDD zai kaɗa ƙuri’a kan ƙudirin tsagaita wuta a Gaza ranar Talata.

Kenya ta ƙulla gagarumar yarjejeniyar tattalin arziki da Turai.

Jagoran gwamnatin sojin Nijar ya yi alkawarin gabatar da jawadalin mika mulki ga farar hula.

Nottingham Forest za ta nada tsohon kocin Wolves da Tottenham Nuno Espirato a matsayin kocinta, inda zai maye gurbin kocin kungiyar na yanzu Steve Cooper.

Daraktan Manchester United John Murtough na Saudi Arabia domin tattaunawa kan cinkin Sancho Varane da Martial, da kuma Casemiro.

Laliga: Girona ta sami nasara akan Deportivo Alves da ci 3:0 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *