Takaitattun Labaran Duniya Na Yammacin Asabar 16/12/2023 – 03/06/1445AH

best seller i

Daga Baba Usman Gama

Shugaba Tinubu yayi ta’aziyar rasuwar tsohon ma’aikacin muryar Amurka Kabiru Fagge.

Sojoji sun ta tabbatar da kashe shahararren dan bindiga Ali Kachalla da kanin Dogo Gide mai suna Machika, da wani mai hada musu bama-bamai da yaransu 36.

INEC ta kwashe takardun zaɓen jihar Kogi daga Lokoja.

Fusatattun matsa sun kori jami’an kwana-kwana da suka je kashe gobarar da ta tashi a kasuwar yankin Road Block da ke Jalingo, babban birnin Jihar Taraba.

Jami’an tsaro sun damke wani dalibi a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Jihar Bauchi dauke da bindiga da harsashi.

Rundunar ƴan sanda reshen birnin tarayya Abuja ta kama wasu hatsabiban ƴan fashi da makami da ta jima ta nema ruwa a jallo.

Jagoran jam’iyyar NNPP Rabiu Musa Kwankwaso, ya ziyarci mutanen da harin bam na Tudun Biri ya shafa, a Asibitin Koyarwa na Barau Dikko da ke Kaduna ranar Asabar.

Bayan ganawa da Kwankwaso Hon. Abdulmumin Jibrin ya zauna da Bola Tinubu kuma sun tattauna game da batun siyasar jihar Kano.

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya zargi jam’iyyar PDP da neman fitina a jihar.

Wata yar Najeriya, Dr Olusimbo Ige, ta kama aiki a matsayin kwamishina a sashen kula da lafiyar jama’a na Chicago a kasar Amurka.

Sarkin Kuwait, Sheikh Nawaf al-Ahmad al-Jaber al-Sabah ya rasu yana da shekaru 86 a duniya.

’Yan Isra’ila sunyi bore kan yadda sojojinsu suka kashe ’yan kasarsu da ke hannun kungiyar Hamas bisa kuskure.

An ayyana hutun kwana 40 domin alhinin mutuwar Sarkin Kuwait.

‘Yan tawayen Houthi sun kai wa garin Eilat na Isra’ila hari da jirage marasa matuƙa.

Kotun Vatican ta ɗaure tsohon mashawarcin Fafaroma shekara biyar.

Kotu ta umarci tsohon lauyan Trump ya biya dala miliyan 148 kan ƙaryar zaɓe.

EPL: Newcastle ta sami nasara akan Fulham da ci 3:0 a wasan yau.

EPL: Manchester City da Crystal Palace sun tashi 2:2 a wasan yau.

EPL: Chelsea ta sami nasara akan Sheffield United da ci 2:0 a wasan yau.

Laliga: Athletic Club ta sami nasara akan Atletico Madrid da ci 2:0 a wasan yau.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *