Daga Baba Usman Gama
Shugaba Tinubu ya jaddada bukatar murkushe ta’addanci a Arewa maso Gabas da ma Najeriya baki daya. Ya bayyana haka ne a yayin bude taron shekara-shekara na Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya a Maiduguri.
Dakarun Rundunar Sojin Kasa sun ceto mutane 9 da aka sace tare da kwato makamai a Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.
’Yan fashi sun kashe mai gadin cibiyar lafiya da ke kauyen Piri a Karamar Hukumar Kwali a Abuja, sannan suka sace janareta kirar Mikano.
Daliban jami’ar da aka sace a jihar Nasarawa sun kubuta.
PDP ta nemi INEC ta gudanar da sabon zabe don cike gibin da ta ce an samu bayan sauyin sheka da wasu ‘yan majalisar dokoki a jihar Ribas suka yi.
Hukumar KAROTA ta bankado wani sabon salo da direbobi suka kirkira wajen shigo da barasa cikin Jihar Kano.
Dakarun Sojin Sama na Operation Hadin Kai (OPHK) sun tarwatsa wani babban rumbun ajiye makamai na ’yan ta’addar Boko Haram a Borno.
Majalisar dinkin duniya zata sake shirya taron kada kuri’ar tsagaita wuta a Gaza.
Gwamnatin Ghana ta dakatar da shugabannin sakandare kan zargin cin hanci.
’Yan wasan Najeriya, Victor Osimhen da Asisat Oshiola sun lashe kambun gwarazan ’yan wasa Afirka na 2023 a bangare maza da mata.
Manchester United na son musayar ɗan wasanta Jadon Sancho, da ɗan wasan Barcelona Raphinha.
Manchester United a shirye take ta sayar da ɗan wasanta Casemiro, da Raphael Varane, da Donny van de Beek da Martial da kuma Sancho.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp