Daga Baba Usman Gama
Hedikwatar tsaron Najeriya DHQ ta bayyana cewa dakarun Najeriya sun kama ‘yan ta’adda 304, sun kama barayin mai 152 sannan sun kashe wasu 80 a makon jiya.
Jami’an tsaron DSS sun kama wani malami kan zargin yi wa dalibarsa ’yar aji biyu a karamar sakandare fyade da har ta dauki ciki a Jihar Osun.
Ministan Ayyuka, David Umahi ya ce Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bar bashin Naira tiriliyan 1.5 a ma’aikatar.
Wani matashi da ake zargi mai damfara ta intanet (Yahoo) ne a jihar Ondo ya kashe makwabciyarsu a gidan haya matashin mai shekaru 25 ya sanya gawarta a cikin jakar Ghana-Must-Go, ya kai wani kango ya boye.
Malam Salihu S. Abubakar ya zama sabon Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna.
Muhammadu Sanusi II ya roki shugabannin kungiyar ECOWAS su gaggauta janye takunkumin da ke kan Nijar.
Hamas ta ce mayakanta sun kashe sojojin Isra’ila 40 cikin awanni 48.
ECOWAS ta nada kwamiti na shugabanni 3 da zai tattauna da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar kan mayar da mulki hannun farar-hula sannan ya duba yiwuwar janye takunkuman da aka kakaba wa kasar.
Ɓangarorin yaƙin Sudan sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta.
Qatar tace suna ci gaba da yunƙurin ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.
EPL: Tottenham ta sami nasara akan Newcastle da ci 4:1 a wasan jiya.
Laliga: Girona ta sami nasara akan Barcelona da ci 4:2 a wasan jiya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp