Takaitattun Labaran Duniya Safiyar Asabar 02/12/2023 – 18/05/1445AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Dakarun sojoji tare da haɗin gwiwar jami’an DSS, sun cafke shugaban ƙungiyar ISWAP na shiyyar Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma.

Tirka-tirkar da ke faruwa a jihar Kano kan shari’ar gwamnan jihar ta dauki wani sabon salo, yayin da APC ta tura wani korafi tare da neman Majalisar dinkin Duniya ta binciki Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Ginin da ke dauke da ofishin shugabanni da ma’aikatan jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ya kama da wuta a ranar Juma’a.

Wani dan dako da baro ya kashe wani mai karbar haraji akan naira 50 a Benin City, jihar Edo kafin daga bisani ya kashe kanshi.

Wani yaro dan shekara 18 Mubarak Akadiri, ya kashe tsohuwar shugabar makaranta, Misis Sidikat Adamolekun, bayan sace wayarta mai darajar naira dubu 66 a jihar Ondo.

Jami’an rundunar yan sandan jihar Ekiti sun kama wani fasto, Abiodun Sunday kan zargin kisan matarsa, Tosin Oluwadare.

Babbar kotun Tarayya ta kori Gwamnatin jihar kano kan zargin kisan kai da ya ke yi wa Alhassan Doguwa kotun yayin hukuncin tayi fatali da korafe korafen yayin da ta umarci Gwamnatin ta biya diyyar miliyan 25 saboda kokarin bata suna.

CBN ya sanar da aniyar kulle asusun bankunan jama’a da ba su da lambobin BVN da NIN nan da Aprilun 2023.

Sarkin Ilorin ya ce bai taba zuwa ya roki EFCC ta kyale wani da ake tuhuma da cin amanar ƙasa ba.

Majalisar dinkin Duniya tacea n samu raguwar mace-mace ta dalilin Ƙanjamau, ‘AIDS’ da kashi 70 a duniya.

Ofishin Majalisar dinkin Duniya tare da hadin gwaiar Tarayyar Turai da sauran takwarorinsu sun kamala wani shirin yaki da cin zarafin mata a Najeriya.

Ƙungiyar Mayaƙan Hezbollah da ke Lebanon ta harba makamai kan dakarun Isra’ila da ke kan iyakar ƙasar, bayan da Isra’ila ta koma kai hare-hare a Gaza.

Ƙarin ƴan Isra’ila biyu da ake garkuwa da su a Gaza sun mutu.

Kasar Benin ta kaddamar da sabbin lambobin yabo don karrama sojojin da suka yi bajinta.

Ministocin kasashen wajen Burkina Faso da Mali da Nijar ranar Juma’a sun bayar da shawarar kirkiro tarayyar kasashen uku a wani bangare na hada kan kasahen don su zama a dunkule wuri daya.

Mahukunta sunce ‘Onana ne gola na biyu mafi bajinta a Premier a bana’.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *