Tinubu ya shawarci gwamnonin APC kan sanya muradun jama’a a gaba

FB IMG 1700890281094 edit 57980466034380

Da zarar al’ummar Najeriya da damuwarsu ta zama jigon tsare-tsare da ayyukanku, ba wai kawai mulki zai yi muku sauki ba, za ku inganta kimar jihohin ku, kuma talakawan jama’a za su samu sabbin damarmaki na bunkasa.

Alfijir Labarai ta mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale, ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Juma’a

Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, da gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, da kuma zababben gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, a Abuja.

A cewar sanarwar, Tinubu ya kara da cewar, kun yi aiki tukuru domin wannan nasarar tawa, don haka Ina alfahari da ku, amma ainihin ƙalubalen ya fara ne kawai.

Wannan shine kalubalen shugabanci nagari, tabbatar cewa kowa yana tafiya tare. Yanzu ku bayin mutane ne. Godiya ta tabbata ga Allah, kuma Allah yayi muku jagora.

Da zarar al’ummar Najeriya da damuwarsu ta zama jigon tsare-tsare da ayyukanku, ba wai kawai mulki zai yi muku sauki ba, za ku inganta kimar jihohin ku, kuma talakawan jama’a za su samu sabbin damarmaki na bunkasa.

Hakazalika more sabon matsayin rayuwa dole ne ya zama abin da kuka fi mayar da hankali a kai a matsayinku na gwamnoni, musamman a matsayinku na gwamnonin da aka zaba a babbar jam’iyyarmu ta APC.

Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇

https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI

Za mu yi aiki tare da ku a matakai na kasa da kasa, kuma za mu tabbatar da karfi da kyakykyawan matsayi in ji shugaban.

A cewar sanarwar, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, wanda ya jagoranci zababbun gwamnoni da jiga-jigan jam’iyyar APC wajen ganawa da shugaba Tinubu.

Ya ce ‘yan takarar jam’iyyar sun gudanar da kan su da gaskiya kamar yadda shugaban kasa ya umarce su a lokacin zabe.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *