Wasu majiyoyi dai sun yi zargin maharan sojoji ne suka kai harin daukar fansa kan hedikwatar rundunar kan kisan wani hafsan soja da wani dan sanda ya yi.
Alfijir Labarai ta rawaito maharan dauke da muggan makamai sun kai hari kan hedikwatar ’yan sanda da ke Jihar Adamawa
Ƙarar sautin harbe-harben maharan a cikin dare ya jefa mazauna garin Jimeta da ke Karamar Hukumar Yola ta Arewa a jihar cikin tashin hankali.
Kakakin ’yan sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya tabbatar wa Aminiya cewa hedikwatar rundunar ce aka kai wa hari, kuma ba a kai ga gano maharan ko manufarsu ba.
Sai dai ya bayyana cewa jami’an rundunar sun yi nasarar fatattakar maharan, bayan musayar wuta ta kusan minti 30 da misalin karfe 11 na daren Talata.
Wasu majiyoyi dai sun yi zargin maharan sojoji ne suka kai harin daukar fansa kan hedikwatar rundunar kan kisan wani hafsan soja da wani dan sanda ya yi.
Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇
https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI
Kawo yanzu dai ana bincike domin gano hakikanin abin da ya faru.
Aminiya
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp