Takaitattun Labaran duniya na Yammacin Talata 21/11/2023CE – 06/05/1445AH

best seller i

Daga Baba Usman Gama

Tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya ce ba don rufe iyakar Najeriya da Nijar da aka yi ba, da tuni ya bar Najeriya ya san inda dare ya yi masa.

Obasanjo ya soki hukuncin kotu kan shari’ar zaɓen gwamnoni.

Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar zaben Gwamna Fintiri na jihar Adamawa.

Rundunar ‘yan sanda ta tsaurara tsaro yayin da ake dakon yanke hukuncin shari’ar zaben jihar Nasarawa.

Rikici ya barke a zauren Majalisar Datttawa kan nadin sabbin shugabannin masara rinjaye a ranar Talatar nan.

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin samar da makamashi mai tsafta na dala miliyan 500 a yankin Tokarawa dake Kano.

Kungiyar ma’aikatan Majalisar Gombe ta janye yajin aikin da ta shiga domin bai wa gwamna Muhammad I. Yahaya damar mika kasafi kudi.

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Filato, Moses Thomas Sule, da mataimakinsa Gwottaon Fom sun yi murabus daga mukamansu.

Hukumar sibil difens, ta kama wasu mutane 27 kan zargin su da zama mambobin kungiyoyin asiri a Jihar Nasarawa.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, ta ce an gano karin gawarwakin mutum bakwai bayan kwanaki bakwai da suka yi hatsarin Kwale-kwale.

Isra’ila da Falasdinawa na tattanawa kan yiyuwar musayar fursunonin yaki da tsagaita wuta don samun damar shiga da kayan agaji a Zirin Gaza.

Mutum 37 sun mutu’ a turmutsutsun da aka yi a wajen daukar aikin soji a Congo.

Kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon ta dauki nauyin wani hari da aka kai kan wasu gidajen da sojojin Isra’ila ke zama a arewacin Isra’ila.

Kungiyar kare hakkokin ‘yan jaridu ta CPJ tace an kashe ‘yan jaridu 53 a yakin Gaza.

‘Yan awaren Kamaru sun hallaka mutum 9 a Arewacin kasar.

Shugaban Afrika ta Kudu Ramaphosa ya zargi Isra’ila da kisan kare dangi a Gaza a taron BRICS.

Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇

https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI

Sabon rikicin iyakar Sudan da Sudan ta Kudu ya hallaka mutane 32.

Dakaraun RSF sun kara kama wani sansanin sojin Sudan.

Mota ta kashe mutum 10 da ke murnar lashe zaɓen shugaban Laberiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *