Hukumar ta ce Jesse na amfani da sunan wani sojan Amurka Devaun Smith Wayne domin damfarar jama’a.
Alfijir Labarai ta rawaito hukumar da ke Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Nijeriya Zagon Kasa, EFCC, ta ce kotu ta yanke wa wani matashi hukuncin zaman gidan yari na shekara biyu kan samun shi da laifin yi wa rundunar sojin Amurka sojan-gona.
Mai Shari’a Darius Khobo na Babbar Kotun Kaduna ne ya yanke masa hukunci bayan wanda ake zargin ya amsa laifinsa guda daya da ake zarginsa da aikatawa.
Bayan yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekara biyu, Mai Shari’a Khobo ya ba shi zabin biyan tarar naira 150,000.
Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇
https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI
Sannan alkalin ya bayar da umarnin kwace wayar Kassah wato Samusng Galaxy A02 wadda ya yi amfani da ita domin aikata laifin.
Fake American Soldier Bags Two Years Jail term in Kaduna
The Kaduna Zonal Command of the Economic and Financial Crimes Commission, EFCC, on Monday, November 20, 2023 secured the conviction and sentencing of Jesse Joshua Kassah, (alias Devaun Smith Wayne) to two years… pic.twitter.com/Eu5R94cJbz
— EFCC Nigeria (@officialEFCC) November 20, 2023
Reshen hukumar EFCC na Kaduna ne ya shigar da Jesse Joshua Kassah kara a gaban kotu bayan an kama shi a yankin Karji na jihar kan zargin damfara.
Hukumar ta ce Jesse na amfani da sunan wani sojan Amurka Devaun Smith Wayne domin damfarar jama’a.
Zamba cikin aminci da yaudara na daga cikin manyan abubuwan da hukumar ta EFCC ke yaki da su a Nijeriya.
Ko a kwanakin baya sai da hukumar ta EFCC ta kama wani matashi wanda ake zargi da yi wa matar Sarkin Bichi zambar miliyan 20.
TRT Afrika
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp