Gawuna ya samu nasara a kotun ɗaukaka ƙara.
Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da zaɓen gwamna Bala Mohammed na Bauchi.
Gwamnatin Kano zata daukaka kara Kotun Koli bayan an ayyana nasarar Nasiru Yusuf Gawuna.
Rundunar soji sun kashe ƴan bindiga shida da suka addabi mazauna karamar hukumar Birnin Gwari tare da kwato makamai a jihar Kaduna.
Gwamna Dauda Lawal na Zamfara ya bayyana hukuncin kotun ɗaukaka kara a matsayin koma baya na wucin gadi.
Dan PDP daya tilo a Majalisar Dokokin jihar Yobe ya koma APC.
Kotun ta bayar da umarnin tsare tsohon Gwamnan CBN, Godwin Emefiele a gidan yari.
Gwamna Adeleke na Jihar Osun, ya umarci ilahirin ma’aikatan jihar su riƙa yin shigar anko na ɗinkin zanin adire zuwa wurin aiki ranakun Laraba.
Hukumar zabe ta INEC ta mika satifiket ga sabon gwamnan jihar Kogi a yau Juma’a.
Isra’ila ta amince a shigar da man fetur zuwa Gaza.
Zimbabwe ta ayyana dokar ta-ɓaci kan cutar kwalara.
Wasu ma’aikata 40 sun maƙale bayan ruftawar hanya a Indiya.
Maza dubu ashirin sun tsere wa Ukraine don guje wa shiga aikin soja.
An binne sojar Isra’ila da aka gano gawarta a Gaza.
Gwamnatin sojin Nijar ta kaddamar da sabon hukumar yaki da rashawa.
Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇
https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI
Ƴan sanda sun yi arangama da masu zanga-zanga a Sifaniya.
Sanannen mawaƙin gambara na Amurka, Snoop Dog wanda ya yi ƙaurin suna wajen shan wiwi ya ce ya daina shan ganye a yanzu.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp