Daga Baba Usman Gama
INEC tace ba za a sake zaɓen gwamnan Kogi a rumfunan da aka dakatar ba.
’Yan sandan sun kama wata mata mai shekara 51 kan zargin satar wata yarinya ’yar shekara uku a garin Minna na Jihar Neja.
Rundunar ‘yan sanda a Legas ta bazama neman wani da ya yi ajalin wata mata a coci.
Gwamnatin tarayya ta na son ganin Sarakai sun samu rawar da za su taka a kundin tsarin mulkin kasa.
Dan takarar gwamna na Jam’iyyar SDP a Jihar Kogi, Muritala Ajaka, ya zargi Hukumar Zabe Kasa (INEC) da magudi a zaben na ranar Asabar.
An kama mutum 5 da ake zargi da yi wa Alkali dukan kawo wuka a Gombe.
Usman Ododo na APC ya lashe zaɓen gwamnan Kogi.
INEC ta ɗage karɓar sakamakon Bayelsa zuwa gobe Litinin.
Tsohon Firaministan Cote d’Ivoire, Guillaume Soro, wanda aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai sakamakon samun sa da laifin zagon kasa ga tsaron kasar, ya ce ya kawo karshen zaman gudun hijira da ya fara a 2019.
Masu zanga-zangar adawa da Isra’ila a Amurka dauke da jerin sunayen Falasdinawa sama da 11,000 da Isra’ila ta kashe a Zirin Gaza.
An rufe manyan asibitocin Gaza biyu saboda hare-haren Isra’ila.
EPL: Chelsea da Manchester City sun tashi 4:4 a wasan jiya.
Laliga: Barcelona ta sami nasara akan Deportivo da ci 2:1
Laliga: Atlentico Madrid ta sami nasara akan Villarreal da ci 3:1 a wasan jiya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp