Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada dan jarida Barr. Abdulsalam Mohammed a matsayin mataimaki na musamman.
Alfijir Labarai ta rawaito Sanarwar ta ce Barr zai yi aiki a matsayin mataimaki na musamman a ofishin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima.
Sanarwar da aka fitar ta hannun sakataren gwamnatin tarayya Sen. George Akume a ranar Juma’a, ta bayyana cewa Barr. Abdulsalam Mohammed ya fara aiki ne daga ranar 20 ga Oktoba, 2023, tare da tsawon shekaru hudu.
Bisa ga wannan nadin, Barr. Abdulsalam Mohammed yana da alhakin kulawa da daidaita ayyukan gudanarwa a cikin ofishin uwargidan mataimakin shugaban kasa, yana ba da gudummawa ga ingantaccen aiki na yankin mataimakin shugaban kasa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp
Good job shugaban kasa