Makarantar ma ahad Idrissiya Islamiyya dake unguwar Rijiyar Lemo a kano, sun gudanar da saukar Al’qur’ani mai girma ga dalibai 41, karo na 6.
Alfijir Labarai ta rawaito makarantar ta yaye dalibai 200, a fannin koyon sana oi daban-daban, kama da hada jakunkuna da Takalma, Dinkin mata da kuma kwalliyar mata.
Shugaban Makarantar Malam Abdullahi ya bayyana godiyar su ga Allah da wadannan Nasarorin da suke samu.
Ya kara da kira ga ɗalibai da su jajirce wajen mai da hankali akan abinda ake koya musu, domin hanya ce mai bullewa duniya da lahira.
Haka ya kara kira ga iyaye kan cewar su daure wajen basu hadin kai wajen turo yaran akan lokaci da kuma biyan dan abin da suke bayarwa na gudanar da makarantar.
Ɗalibai da dama sun nuna farin cikinsu musamman na saukar Al’qur’ani mai girma, sannan kuma ga sana oi da suka koya kala kala, kamar yadda Wakiliyar Alfijir Labarai Ruƙaiyya Umar Gadon kaya ta tattauna dasu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp