Ibtila’i: Gobara ta kone Shahararriyar Shagon Samsung Dake Banex Plaza A Birnin Tarayya Abuja

FB IMG 1699307390194 edit 25071746005548

Kawo yanzu dai babu cikakken bayani kan musabbabin tashin gobarar ko kuma adadin wadanda suka mutu har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Alfijir Labarai ta rawaito cewa an samu tashin gobara a ranar litinin a ofishin Samsung daks Banex Plaza kusa da Aminu Kano Crescent a Wuse II, Abuja.

A cikin wani faifan bidiyo da wakilinmu ya samu, an ga shahararren shagon sayar da kayan lantarki a cikin wuta yayin da aka ji wasu mutane na kururuwa a bayan fage.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, wakilinmu ya tabbatar da cewa, tuni jami’an hukumar kashe gobara ta birnin tarayya Abuja suka yi mai yiwuwa wajen kokarin shawo kan gobarar.

“Eh, gaskiya ne. Tuni mutanen mu suna nan a kasa,” Shugaban ayyuka na Hukumar kashe gobara ta Abuja, Abiola Adebayo, ya shaida wa manema labarai.

Kawo yanzu dai babu cikakken bayani kan musabbabin tashin gobarar ko kuma adadin wadanda suka mutu har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

FB IMG 1699307394479
Samsung Office Abuja

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *