Daga Baba Usman Gama
Majalisar Dattijawan Najeriya ta amince Tinubu ya ciwo bashin dala biliyan 7.8.
Rundunar ƴan sandan jihar Imo ta musanta cewa jami’anta sun kama shugaban ƙungiyar ƙwadago, Kwamared Joe Ajero a garin Owerri.
Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya yi umurnin cewa gaba daya rassan hukumar su daina kai samame cikin dare.
Rundunar yan sandar jihar Yobe tace Boko Haram ta kashe aƙalla mutum 40 a jihar.
Shugaban Ma’aikatan Kano, Alhaji Usman Bala ya yi murabus daga muƙaminsa.
Kansiloli 9 sun tsige Shugaban karamar hukumar Kaura a jihar Kaduna.
Jam’iyyar NNPP ta yi galaba a kan APC a Kotun daukaka kara a kan shari’ar zaben ‘dan majalisar Kumbotso Mannir Babba Dan’agudi.
Kotun a jihar Ribas ta ba da umurnin wucin gadi na hana majalisar dokokin jihar Ribas da kakakin majalisar, Martin Amaewhule tsige gwamnan jihar, Siminalayi Fubara.
’Yan sanda sun cafke wasu masu gadi kan zargin hadin baki da kuma yi wa wata karamar yarinya yar 12 fyade a yankin Kirikiri da ke Jihar Lagas.
Akalla dalibai 70 ne jami’an hukumar EFCC suka cafke a Ile-Ife bisa zargin su da aikata laifukan damfara a intanet saidai kungiyar daliban jami’ar Obafemi Awolowo ta gudanar da zanga-zanga a ofishin hukumar EFCC na shiyyar Ibadan dan neman sakin daliban.
Sojojin Isra’ila da aka kashe a Gaza sun kai 16, inji ta.
Adadin mutanen da suka tsallaka Masar daga Gaza ya kai 400.
Sojoji sun kaddamar da babban bututun danyen mai daga Nijar zuwa Benin.
EFL: Newcastle ta sami nasara akan Manchester United da ci 3:0 a wasan jiya.
EFL: Westham ta sami nasara akan Arsenal da ci 3:1 a wasan jiya.
EFL: Liverpool ta sami nasami nasara akan Bounemouth da ci 2:1 a wasan jiya.
EFL: Chelsea ta sami nasara akan Blackburn da ci 2:0 a wasan jiya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp