Daga Baba Usman Gama
Shugaba Tinubu ya ce jami’an gwamnatinsa da ya nada dole ne su zage damtse su yi aiki tukuru don cimma muradun ‘yan Najeriya.
CBN ya ce har yanzu takardun tsofaffin kuɗi na N200, N500 da N1000 za su cigaba da zama a matsayin halastattun kuɗi har bayan ranar 31, ga watan Disamban 2023.
EFCC ta cafke daliban Jami’ar Obafemi Awolowo 70 a daren jiya Talata a jihar Osun.
Masu zanga-zanga a zauren majalisar sun riƙa rera waƙoƙin haɗin kai kana suka ɗaga tutoci masu rubutu daban-daban kamar, “A kori Bello Matawalle yanzu.”
Kotu ta yanke wa wanda ya watsa wa budurwarsa ruwan batir daurin rai da rai a jihar Cros River.
Gwamnatin tarayya ta na shirin batar da N1.5bn a kan motocin da za a rika amfani da su a ofishin uwargidar shugaban Najeriya.
Kotun ɗaukaka ƙara ta ƙwace kujerar sanatan Benue ta Arewa maso Gabas daga hannun Suswam na PDP inda ta miƙa ta a hannun ɗan APC.
Kotu a Abuja ta baiwa Godwin Emefiele, wa’adin daga nan zuwa ranar 25 ga watan Janairu, 2024 ya bayyana a gabanta.
Kotun sauraran kararrakin zabe a jihar Plateau ta tabbatar da nasarar Sanata mai wakiltar Plateau ta Tsakiya, Diket Plang na APC.
Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Kamilu Abdulkarim a majalisar tarayya ta Wudil/Garko daga jihar Kano.
Gwamnatin tarayya ta raba tallafin kuɗi ga ɗalibai mata na jami’ar tarayya da ke Gusau waɗan da aka ceto daga hannun ƴan bindiga.
Jami’an tsaro sun kama shugaban Kungiyar Kwadago (NLC), Joe Ajaero a Owerri babban birnin jihar Imo.
An bude iyakar Masar ga Falasdiwa da suka jikkata da baki a karon farko.
Kasashen Latin sun fusata da Isra’ila bayan kashe ‘yan gudun hijira a Gaza.
‘Yan tawayen Mali sun mamaye sansanin dakarun MDD.
Kasar Bolivia ta yanke hulda da Isra’ila a kan yakin Gaza.
Kotun Iran ta yanke wa matar aure hukuncin kisa bisa laifin ‘bin maza’.
WHO ta yi maraba da matakin Masar na karɓar marasa lafiya daga Gaza.
Al’ummar Kenya sun fusata kan sabon harajin kaya ga matafiya.
An ɗaure wanda ya kitsa juyin mulkin Gambia shekaru 12 a gidan yari.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp