Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da Natasha a matsayin zaɓaɓɓiyar Sanatan Kogi-ta-Tsakiya
Alfijr Labarai ta rawaito Kotun daukaka kara da ke Abuja, a yau Talata, ta tabbatar da nasarar Natasha Akpoti-Uduagan ta jam’iyyar PDP a matsayin wacce ta lashe zaben Sanatan Kogi-ta-Tsakiya da aka gudanar a watan Fabrairu.
Kwamitin mai mutane uku, a hukuncin da ya yanke, ya amince da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar tare da yin watsi da karar da Sanata Abubakar Ohere na jam’iyyar APC ya shigar.
Kotun ta amince da hujjojin da lauyan Akpoti-Uduagan, Joshua Usman, SAN, ya gabatar saboda sun inaganta.
Kotun daukaka karar ta kuma ci Ohere tarar Naira dubu N500,000.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp