Takaitattun Labaran duniya na Safiyar Laraba 25/10/2023 – 10/04/1445AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Kwamitin shugaban kasa yace karbar haraji daban daban shine dalilin durkushewar masana’antu a fadin kasa.

Sojoji sun kashe ‘yan fashi da dama a jihar Sokoto

Fadar Sarkin Fika ta ayyana karfe 4 na yamma matsayin lokacin jana’izar Wazirin Fika, Malam Adamu Fika, wanda ya rasu yana da shekara 90 a duniya.

Kotun Majistare mai lamba 60 da ke Nomansland a Jihar Kano ta gurfanar da dan siyasar nan, Anas Abba Dala gabanta bisa zargin yin barazanar duka ga Malam Lawal Abubakar Limamin Masallachin Juma’a na Triumph.

Shugaban Hukumar EFCC ya bukaci dukkan jami’an hukumar su bayyana kadarorinsu.

Kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta dauki matakin shari’a domin kakaba takunkumi kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar.

Harin ta’addanci ya hallaka mutane kusan 30 a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.

Za a je zagaye na biyu a zaɓen shugaban ƙasar Liberiya.

Kotu a Jamhuriyar Nijar ta wanke janar Souleymane daga zargin yunkurin juyin mulki.

Masu hakar Zinare a Afirka ta Kudu sun makale a ramin hakar Zinare.

Sakataren Majalisar dinkin Duniya Antonio Guterres yace Isra’ila ta shafe shekara 56 tana gallaza wa Falasɗinawa.

Ministan harkokin wajen Isra’ila ya soki Sakataren MDD Antonio Guterres game da kalaman da ya yi.

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da kusan mutum 40 a Kamaru.

Kotun Ghana ta tura ‘yan Kamaru gidan yari kan karya dokar shige-da-fice.

Shugaban Iran yace rashin hadin kan Musulmai ne ya sa Isra’ila ke ci gaba da cin zalin a Gaza.

UCL: Manchester United ta sami nasara akan Kobenhavn. 1 0

UCL: Real Madrid ta sami nasara akan Braga da ci 2:1 a wasan jiya.

UCL: Arsenal ta sami nasara akan Sevilla da ci 2:1 a wasan jiya.

UCL: Bayern Munich ta sami nasara akan Galatasaray da ci 3:1 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KpTjEvHUjd3CVzIQp8CSkZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *