Shugabannin Makarantar Al-Azhar Academy Sun kashe Wani Ɗalibi Sakamakon Dukan Kawo Wuƙa

📸Alfijir Labarai

A ranar Juma’a ne muka samu labarin wani mummunar hukunci da hukumar makarantar Al-Azhar Academy dake bayan Kofar Gayan Zariya suka yi wa wani dalibinsu mai suna Marwanu Nuhu Sambo, dan JS3 (Basic 9), wanda a yayin wannan hukuncin sai da suka aika shi har lahira, saboda tsananin hukunci.

Alfijir Labarai ta rawaito bayan kisan wannan yaro da suka yi, ba su sanar da iyayensa ba har sai da iyayen yaron suka rika jin rade-radin cewa an kai yaron asibitin Al-Ridha Clinic, inda suka garzaya can domin tabbatar da labarin da suke samu game da dan nasu, amma bayan sun samu likitan, sai ya fada masu cewa, shi ba mara lafiya aka kawo masa ba; gawa ce aka kawo masa.

Wakilin Rariya bayyana kai ziyarar sa har wannan makaranta domin tabbatar da wannan labarin, a inda na zanta da wasu dalibai 2 da kuma wani yaro mai sayar da abinci a makarantar, tare da wata mata duka suka tabbatar man da faruwar wannan al’amari.

Daga nan, na garzaya zuwa gidan da dalibin da aka kashe yake, na tattauna da wasu iyayensa guda biyu, duka suka tabbatar man da faruwar abin, har suka kai ni inda ake yi wa gawar yaron wanka.

Bayan nan, na sake zuwa wurin wasu daliban makarantar, inda na zanta da su, daya daga cikin yaran ajinsu dalibin da aka kashe.

Sannan ya labarta man yadda malaman suka aikata wannan hukunci.

Yaron ya ce, mataimakin shugaban makarantar (vice principal) shi ya zo da yaron gaban assembly, inda suka rika yi masa bulala babu kakkautawa tare da shugaban makarantar (Principal), tun suna iya kirga bulalar har suka bata lissafi, inda yaron ya tabbatar man da kansa ya kirga bulala akalla 105 wanda aka yi wa yaron a gaban assembly, daga nan kuma suka wuce da shi office, suka cire masa riga, suka bar shi da gajeren wando kawai, suka ci gaba da dukan sa har yaron ya yi yunkurin gudu, amma aka sa (prefects) na makarantar suka rike shi suka koma da shi, suka ci gaba da dukan sa har sai da suka cire masa hakora, suka kashe shi.

Duk kuma dalilin wannan hukuncin kawai, shi ne ba ya zuwa makaranta kullum.

Bayan sun kashe yaron, suka fito da shi waje, suka aje shi a hanyar bayi har aka tashi makaranta.

Abin da zai kara ba ku mamaki shi ne, har zuwa karfe 8:30 na daren nan da kuma lokacin da nake wannan rubutun, babu wasu hukuma na wannan makaranta da suka halarci gidan wannan iyayen yaron.

Muna kira ga hukuma, da kungiyoyin kare hakkin dan Adam, da hukumar ilmi ta jihar Kaduna da su shiga cikin wannan lamari, domin nema wa wannan dalibi hakkinsa, tare da hukunta wannan makaranta daidai da laifin da ta aikata, domin mun dade muna samun labarin irin mummunar hukuncin da ake yi a wannan makaranta mai suna Al-Azhar, wadda take Kofar Gayan Zariya; sumar da yara dalibai ya zama ruwan dare a wannan makaranta saboda tsananin hukunci.

Rariya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

One Reply to “Shugabannin Makarantar Al-Azhar Academy Sun kashe Wani Ɗalibi Sakamakon Dukan Kawo Wuƙa”

  1. Gaskiya da a Kano wannan Makarantar take da tuni ba wannan labarin Ake ba domin Mutanen Kano ba sa yarda a zuba ido a ci zarafin dalibai, Hakan yasa hukumar ilimin jihar Kano ta hana malamai rike bulala , ya Kamata gwamnatin jihar Kaduna ta rufe wannan Makarantar Sannan malaman da suka aikata haka. Da gan gan su fuskanci hukunci dai dai da abinda da suka aikata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *