Daga Baba Usman Gama
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin ba da tallafin kudi ga magidanta miliyan 15.
An samu rashin jituwa tsakanin Shugaban Majalisar Dattawa da Sanata Ali Ndume yayin wani zama a yau Talata.
Yan bindiga sunyi garkuwa da mata da ‘ya’ya 2 na dan majalisar dokokin jihar Kwara mai wakiltar mazaɓar Ipaiye/Malete/Olooru a jihar.
Dakta Umar Ganduje, shugaban jam’iyyar APC ta kasa na wata ganawar gaggawa da ‘yan majalisun jihar Ondo.
Gwamnatin Sokoto ta kafa kwamitin samar da ƴan sintiri.
Kotu ta ɗaure waɗanda aka kama da ƙoƙon kan mutum a Najeriya.
A makon nan ake sa rai gwamnatin jihar Kano a karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf za ta tura yara karatu zuwa ketare.
Babbar kotun Tarayya da ke Kano ta daure wani Mohammed Bako Sambo daurin shekaru 10 a gidan kaso kan zargin safarar kwayoyi da tabar wiwi.
Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya ba da wa’adin awa 72 a rushe gidajen karuwai da matattarar bata-gari a Maiduguri.
Ƙungiyar ƙasashen Musulmai za ta yi taron gaggawa kan rikicin Gaza.
Iran ta ba Isra’ila wa’adin ficewa daga Gaza ko ta kuka da kanta.
Kungiyar malamai a Zimbabwe tace ƙasar na rasa malamai 300 a kowane wata yayin da suke zuwa ƙasashen ketare domin samun rayuwa mai inganci.
An gano gawawwaki 47 a hatsarin kwale-kwale a Kongo.
Kotu ta ƙi amincewa da buƙatar halasta auren jinsi a Indiya.
Alamu na nuna cewa za a je zagaye na biyu a zaben shugaban kasar Liberia.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo