Daga Baba Usman Gama
Shugaba Tinubu zai yi zama da ministocinsa da sauran manyan jami’an gwamnatin tarayya a taron FEC.
Mukaddashin Sufeto-Janar na ‘yan sanda zai jagoranci tawagar manyan jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya zuwa taron kungiyar shugaban nin ‘yan sanda na kasa da kasa na 2023 a San Diego, Carlifornia, Amurka.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya ce zai iya sadaukar da rayuwarsa domin kawo karshen matsalar ‘yan bindigar da suka addabi jiharsa.
Ƴan bindiga sun halaka mutum 3 a wani sabon hari da suka kai a ƙauyen Imaton a cikin Gaambe-Tiev na ƙaramar hukumar Logo ta jihar Benue.
Iran ta gargadi Isra’ila kan shirinta na mamaye Zirin Gaza.
‘Yan sandan Uganda sun dakile wani harin bam na kungiyar ADF.
Kotun Gabon ta sallami Mike Jocktane da Thérence Gnembou.
Falesdinawa na samun goyon baya daga Kasashen Duniya.
Masar ta gabatar da tsarin gayyato taro na samar da sulhu a rikicin Isra’ila da Falesdinu.
Fafaroma Francis ya nemi a buɗe ƙofofin kai agaji a Gaza.
Dimbin mutane a birnin Amsterdam na kasar Netherlands sun bi sahun sauran kasashen duniya wajen gudanar da gangamin nuna goyon baya ga Falasdinawa.
PSG za ta gabatar wa Kylian Mbappe tayi na ƙarshe na sabunta kwantiraginsa, yayin da Real Madrid ke dakon ganin abin da zai biyo baya.
Bisa ga dukkan alamu akwai sauran magana a game da yuwuwar sayen hannun jari na kashi 25 cikin ɗari da Jim Ratcliffe zai yi a Manchester United, kuma wataƙila maganar ta yi tsawo sosai.
Turkiyya ta samu gurbin zuwa Gasar UEFA EURO 2024 bayan ta doke Latvia 4-0.
Euro Qualify: Spain ta sami nasar
akan Norway da ci 1:0 a wasan jiya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo