Daga Baba Usman Gama
Majalisar dattawa za ta yi ƙudurin cin tarar iyayen da suka ƙi kai ‘ya’yansu makaranta.
Najeriya ta janye takunkumin hana shigar mata da kayayyakin masarufi 43.
Sojojin Najeriya sun halaka ‘yan ta’adda fiye da 100 a jihar Zamfara.
Mutum 6 sun kone kurmus a Jos, babban birnin Jihar Filato bayan wata gobara da ta tashi sakamakon fadowar wayar wutar lantarki.
Gwamnatin Kano ta baiwa wani karamin ma’aikaci kujerar Hajji da daukar aiki dindindin da kyautar miliyan 1, saboda mayar da miliyan 16 da ya tsinta a harabar Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar.
Gwamnan jihar Ogun ya rantsar da sabbin kwamishinoni da masu ba shi shawara.
An kama mutum uku da ‘wayoyin sata’ 318 a Kano.
Gwamnatin Kano ta shirya wa amaren da ta aurar walima.
Shugaban Hamas ya zargi Isra’ila da aikata laifukan yaki a Gaza.
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ce shi da majalisar ministocinsa suna tare da Falasdinawa dari bisa dari.
Kotu ta maida jagoran ‘yan adawar Senegal cikin ‘yan takarar shugaban kasa.
An yi zanga-zangar goyon bayan Falasdinu a birnin New York na Amurka.
Ƙatar da Saudiyya kai tsaye sun yi watsi da umurnin tayar da ‘yan Arewacin Gaza.
Faransa ta haramta zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a Paris duk da cewa an gudanar da makamanciyarta domin goyon bayan Isra’ila a wasu birane na kasar.
Ronaldo ya ci kwallonsa ta 857 a wasan da kasarsa ta Portugal ta buga da Slovakia inda aka tashi 3-2.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo