Shaidu sun ce matashin ya kuma yi wa mahafiyar tasa mai shekaru 65 mummunan sara a kanta, sannan ya yayyanke ta a kafarta da wasu sassan jikinta.
Alfijir Labarai ta rawaito wanda ake zargin ya yi wa datijuwar wannan aika-aika ne a kauyne Akibo da ke Karamar Hukumar Obafemi Owode ta Jihar Ogun.
A cikin daren ranar Laraba ne aka ji hayaniya a gidan tsohuwar, inda makwabta suka je domin kai dauki, amma ko da suka isa, sai suka same ta cikin jini, da hannuwanta biyu duk an datse su, da kuma sara a kanta, shi kuma dan nata yana tsaye a kanta ya rike wata sharbebiyar adda.
Jaridar Punch ta bayyana wani makwabcinsu yana cewa wanda ake zargin ya kuma sari mahaifiyar tasa a kafa da wasu sassan jikkinta, amma an kaita asibiti domin ba ta kulawa.
Kakakin yan sandan jihar Ogun, Omolola Odutola, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce rundunarsu ta cafke matashin kuma sun fara gudanar bincike kan lamarin.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo