Mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasar da ta faru a yammacin Afghanistan sun zarta 2,000 sannan fiye da 10,000 sun jikkata a yayin da ake kokarin ciro wadanda gine-gine suka rufta a kansu, a cewar kakakin gwamnatin Taliban.
Alfijir Labarai ta rawaito Hukumar kula da yanayi ta Afghanistan ta tabbatar da cewa girgizar kasar, mai karfin maki 6.3 da ta auka wa kasar ranar Asabar, ta kashe mutum 2,053 kawo yanzu. Kazalika ta lalata sama da gida 1,300.
Abdul Wahid Rayan, mai magana da yawun Ma’aikatar Watsa Labarai da Al’adu, ya ce mutanen da suka mutu a yankin Herat sun zarta adadin da aka bayyana da farko.
Girgizar kasar ta lalata kusan kauyuka shida, kuma gine-gine sun danne daruruwan mutane, yana mai yin kira a kai musu agajin gaggawa.
Sai dai kamfanin dillancin labaran kasar Bakhtar News Agency, ya ambato hukumar bayar da agaji ta Afghan Red Cresent tana cewa kauyuka 12 da ke yankunan Zinda Jan Ghorian na lardunan Herat – inda kusan mutum miliyan 1.9 ke zaune – sun lalace “baki daya.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo