Ni Na Nemi Obasanjo Ya Bar Tinubu A 2003 ya zama gwamnan jihar Lagos – In Ji Atiku

Atiku Abubakar ya bayyana wasu zarge-zargen da suka shafe shi da Bola Tinubu, da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a 2007.

Alfijir Labarai ta rawaito Atiku ya bayyana cewa ya roki Obasanjo ya bar Tinubu ya mallaki jihar Legas a 2003 saboda PDP ta kwace yankin Kudu maso Yamma baki daya.

Ya dage kan cewa Tinubu ya yi wa Marigayi Shugaba Umar ‘Yar’adua aiki, inda ya jaddada cewa shi ya lashe zaben fidda gwanin sa da aka gudanar a Legas a shekarar 2007 bisa cancanta.

Dan takarar jam’iyyar PDP na 2023 ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai da ya gabatar a taron jami’ar jihar Chicago da ke Abuja ranar Alhamis.

A cewar Atiku: “Tinubu bai goyi bayana ba a 2007, a zaben fidda gwani da aka gudanar a Legas ba, na yi nasara kawai bisa cancanta.

Daga baya ya aiko min da mutane domin ya zama abokina, amma ba na son tikitin musulmi na musulmi, har yau, ba zan taba goyon bayan hakan ba.

“A shekarar 2007, Tinubu ya yi wa Umaru Musa ‘Yar’aduwa aiki ya yi nasara.

“Duk da cewa ni ne na nemi Obasanjo ya bar masa Legas a shekarar 2003, ya bar masa jihar Legas, duk sauran jihohin Kudu-maso-Yamma muka kwashe amma da gangan muka bar Legas zuwa Tinubu, abin takaici, ya goyi bayan Yar’Adua a kaina.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *