Kansila Hazel Johnson ya ce tubar ba ta buƙatar izinin tsarawa saboda amfani da shi a matsayin wurin ibada bai canza ba
Alfijir Labarai ta rawaito an tabbatar da cewa Cocin Victorian Methodist da aka dade ba a amfani, an amince da maida shi masallaci.
Cocin Methodist na Clayton Heights a Bradford, wanda aka sanar da shirun a shekarar 1870, ya kasance ba a amfani da shi tun shekarar 2020.
A baya an amince da shirin mayar da ginin da ke Layin Chapel zuwa gidaje masu dakuna uku uku, da masu biyu-biyu, amma ba a aiwatar da hakan ba.
Kansila Hazel ya ce a maimakon haka al’ummar musulmin yankin ne suka saye cocin domin a gyara musu masallaci cikin gaggawa.
Ms Johnson, wacce ke wakiltar gundumar Queensbury, ta ce shirin ba ya bukatar izinin tsarawa, saboda amfani da shi a matsayin wurin ibada bai canza ba.
Ta ce “abin mamaki” ne ga Queensbury kuma “ana bukatar masallaci ga musulmai a cikin al’ummarmu”.
Ta ce gaba ɗaya shawarwarin sun sami sakamako mai kyau, duk da cewa ta yarda cewa ta “cika da damuwa” game da wuraren ajiye motoci da ababen hawa, musamman a ranar Juma’a da ake yin sallah sau biyu da rana.
Ms Johnson ta ce sabbin maallaka ginin sun ba da tabbacin cewa, zasu dinga kammala dallaloin kafin tashin yan makaranta.
BBC News
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo