Nuna murnar Maulidi duk yadda kayi, ko kayi taro, ko kayi sallah ko zikiri duk abu daya ne, mutukar ba a kaucewa hanya ba.
Alfijir Labarai ta rawaito Sarkin Hausawan Afirka Sardaunan Agadas, Dokta Abdukadir Labaran Koguna ya bayyana murnarsa da Zagayowar wannan rana da aka haifi fiyayyen halitta Annabi Muhammadu Sallahu Alaihi Wasallim.
Basaraken yace ya kamata duk musulmin kwarai ya nuna murnar sa ko ta wane hali a wannan watan, domin Allah ya halicci duniya ne da lahira domin sa, kaga kuwa ya zama tilas mu nuna murnarmu ga samun fiyayyen halitta.
Shi nuna murnar Maulidi duk yadda kayi, ko kayi taro, ko kayi sallah ko zikiri duk abu daya ne, mutukar ba a kaucewa hanya ba.
Don haka muke kira ga musulmi a duk in da suke da su yawaita yiwa kasa addu a Allah ya kawo mana sauki da rangwame ameen.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb