Ministar yawon bude ido ta Najeriya, Lola Ade-John, a halin yanzu tana kwance a wani asibitin Abuja, sakamakon wani abu da ake ganin kamar guba ne da ba a tantance ba.
Alfijir Labarai ta rawaito ƴan uwanta na fargabar cewa jan lokaci na iya kawo cikas ga yunkurin da suke yi na ceto rayuwarta.
“Lola Ade-John, mai shekaru 60, an garzaya da ita Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya, Jabi, jim kadan bayan ta fara bayyanar da alamun gubar da ta sha, kamar yadda majiyar ‘yan uwa da suka san halin da ta shiga suka bayyana.
Ta shafe kwanaki hudu a wurin har zuwa safiyar Juma’a,” in ji majiyar.
Takamaiman abin da ta sha da kuma yadda ba za a iya gano shi nan da nan ba”.
A cewar rahoton Peoples Gazette, ‘yan sanda da ma’aikatar tsaro ba su mayar da bukatar gaggawa kan lamarin ba.
Ta ci gaba da cewa: “Halin da take ciki ya kara jefa ‘yan uwa da gwamnati cikin damuwa, inda aka ce sakataren dindindin na ma’aikatarta ya magantu kan ko za ta ci gaba da jinya a asibitin gwamnati ko kuma a kai ta wani gida na daban mai inganci, makaman cikin gari.
“An ce sakatariyar dindindin, Ngozi Onwudike, ta dage cewa bai kamata a dauke ministar ba, saboda FMC asibitin gwamnati ne, kuma ayyukanta za su jawo wa gwamnati tuhume-tuhume a kai, lamarin da danginta suka ki amincewa.
Amma dangin sun ci gaba da kasancewa tare da ita a wannan asibitin, saboda ba su da kudin da za a kai ta asibiti mai zaman kansa, inji majiyarmu.
“Mai magana da yawun hukumar ta FMC bai amsa bukatar neman karin bayani kan halin da Ms Ade-John ke ciki.
“Shugaba Bola Tinubu ya nada Ms Ade-John a matsayin minista a watan Agusta.
Nan take aka dauke ta a matsayin daya daga cikin ‘yan majalisar ministocin da aka nada.
Ta kasance a Landan na tsawon shekaru kafin shugaban kasa ya nemi ta koma kasar don yin hidima.”
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb